Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a tace Dalibai zasu iya cire takardar Slip domin zana jarabawar gwaji ta Mock, a matsayin wani yunkuri na fara shirye-shiryen zana jarabawar.
Hukumar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa datake fitarwa duk sati-sati, a ranar Litinin a Abuja.
” Daliban da suka yi rajistar Jarabawar Shekarar 2021 Kuma suke da ra’ayin zana jarabawar gwaji kafin ta ainahi, to zasu iya cire takardar shedar hakan daga ranar Lahadi 9 ga watan Mayu”.
” Wannan wani shirye-shirye ne domin zana jarabawar gwajin da za’a gudanar a ranar Alhamis 20 ga watan Mayu.
“Jarabawar gwajin, za’a iya cire takardar shedar daga ko’ina, ta hanyar adireshin yanar gizo ta https://www.jamb.gov.ng “.
Hukumar ta kara dacewa takardar ta kunshi Dukkanin bayanan Dalibi da suka hada da Lambar rajista, da Kuma inda zasu gudanar da ‘ita, a cikin garuruwan daya zabi zana jarabawar JAMB.
Takardar Slip din, ta kuma kunshi lokacin da ake saran Dalibai zaije wurin da zai zana ta.
Hukumar tace a halin yanzu Dalibai Dubu Dari 845,517 suka yi rajistar zana jarabawar UTME, inda Kuma Dalibai masu neman DE, yawan wadanda suka yi rajista yakai Dubu 38,886, daga jiya Lahadi 9 ga watan Mayu.
Kamfanin Dillacin Labaru na Kasa ya ruwaito cewa rajistar Jarabawar an fara ta ne daga 8 ga watan Afrilu, inda za’a kammala a ranar 15 ga watan Mayu, a yayinda Jarabawar zata fara daga 5 ga watan yuni zuwa 19 ga watan yuni.