Matsalar Tsaro: Masarautar Katsina ta soke shagulgulan Hawan Sallah

Sakamakon yawaitar Matsalar tsaro dake ta kara kamari a Gundumar Masarautar Katsina dama sauran yankuna na Jahar Katsina, Masarautar Katsina ta dakatar da shagulgulan Hawan Sallah Karama, wanda ta saba shiryawa duk Shekara.

Wannan na kunshene a cikin wata sanarwa da Sakataren Masarautar Alhaji Bello Mamman Ifo ya sanyawa hannu aka rarrabawa Manema Labaru.

Masarautar tace sakamakon shawarwari daga Jami’an tsaro da Gwamnati, da Kuma Ma’aikatar Lafiya, ya sanya ta dakatar da shagulgulan hawan Sallar.

Sanarwar ta kuma kara dacewa, za’ayi amfani da lokuttan Karamar Sallah domin gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da lumana a Gundumar Masarautar, Jahar Katsina dama Najeriya baki daya.

Idan ba’a manta ba, a Shekarar data gabata, JARIDAR DIMOKRADIYYA ta kawo maku rahoton cewa Masarautar ta soke hawan Sallah, sakamakon Cutar Covid-19 data fara yaduwa a Jahar, Najeriya dama Duniya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: