DA DUMI-DUMI: Allah ya yiwa Hajiya Jummai Alhassan (Maman Taraba) rasuwa a wannan rana ta Juma’a.
Hajiya Jummai ta rasu ne a Cairo babban birnin kasar Egypt bayan ta yi fama da rashin lafiya.
Kafin rasuwar ta taba zama ministar harkokin mata a Najeriya karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.