‘Yan bindiga sun kashe kwamishina a jihar Kogi.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kashe mista Solomon Adebayo wanda shine kwamishinan kula da harkokin fansho na jihar lokacin da yak e ziyara a wani yanki da ke jihar

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kogi William Ayah ya ce ‘yan bindgar sun bindige mista Solomon Adebayo ne lokacin da yak e kan hanyarsa ta zuwa garin Kabba bayan ya baro birnin Ilorin da ke jihar Kwara da yammacin jiya asabar.

Ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta ga motar kwamishinar ne inda alburusai ya same shi sannan ya mutu nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published.