Sarkin Katsina ya dakatar da hakimi sakamakon zargin sa da alaka da ‘yan bindiga

Masarautar Katsina ta dakatar da hakimin Kankara Alhaji Yusuf Lawal, sakamakon zarginsa da hannu wajen taimakawa ‘yan bindiga a yankinsa.

 

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren masarautar Katsina Alhaji Mamman Iso a madadin Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Usman, ta tabbatar da dakatarawar.

To sai dai sanarwar mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Afrilun jiya ba ta yi cikakken bayanin irin rawar da ya taka wajen tallafawa ‘yan bindigar ba.

 

Sanarwar ta kara da cewa masarautar ta kafa kwamitin bincike don gano gaskiyar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: