NLC: Korar ma’aikata dubu 30 da El-Rufai ya yi shi ya kara ta’azzara rashin tsaro

Gamayyar kungiyoyin ma’aikata sun alakanta rashin tsaro dake addabar jihar Kaduna da korar ma’aikata 30,000 da gwamna Nasir El-Rufai ya yi tun farkon hawansa a shekarar 2015 zuwa yanzu.

 

Sakataren gamayyar kungiyoyin Kwamared Sikiru Waheed ne ya bayyana haka yayin taron bikin ranar ma’aikata a Abuja.

Kwamared Waheed ya ce gamayyar kungiyoyin za su goya wa babbar kungiyar kwadago baya kan duk matakin da za su dauka a kan ma’aikatan jihar Kaduna.

 

Kungiyar ta yi barazanar rufe jihar Kaduna tare tsayar da duk harkokin kasuwanci sakamakon korar ma’aikata dubu-biyar.

 

Ya kara da cewa wannan hukuncin shi ya haddasa rashin tsaro a jihar Kaduna da makwabtan jihohin irin su Niger da Kogi da ma birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published.