An gano ma’aikatan bogi 668 a jihar Gombe – Kwamishina

Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da dakatar da ma’aikata 668 da take zaton na bogi ne sakamakon gaza bayyana a gaban kwamitin tantance ma’aikatan jihar don daukar bayanansu a na’ura wato biometric.

 

Kwamishin kudi da bunkasa tattalin arzikin jihar Muhammad Gambo Magaji ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai kan fara aikin tantancewar.

Muhammad Gambo Magaji ya ce bisa wannan bincike yanzu haka sun samu nasarar alkinta kudi naira miliyan 38 da dubu dari uku, bayan cire sunayen ma’aikatan da suka gaza bayyana.

Ya kuma kara da cewa aikin tantancewar zai ci gaba har sai sun kammala tantance ma’aikatan Jihar baki-daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.