Na Ɗauki Kirista Fiye Da Musulmai A Matsayin Ma’aikata ~ Isa Pantami

 

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Dr Isa Pantami, ya musanta wata alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda ko nuna bambancin kabilanci da na addini, yana mai cewa ya dauki Kiristocin da suka fi Musulmai yawa aiki a matsayin ma’aikatansa.

 

“Direba na Ɗan Keffi ne, mai bin addinin Kirista. Ina kuma da Kirista, Ms Nwosu, a matsayin sakatare na da Dr Femi, Kirista, a matsayin mai ba ni shawara kan harkar fasaha.

 

“Idan ba na son Kiristoci ko kuma ban dauke su a matsayin ƴan uwana maza da mata ba, da ban dade ina aiki tare da su ba. Na dauki Kirista fiye da Musulmai aiki a ma’aikatana saboda na yi imani da cancanta kan kabilanci.

 

“Ban taba amincewa da ta’addanci ba kuma na ki amincewa da duk wata alaka da kungiyoyin ta’addanci. Na dade ina wa’azin zaman lafiya tsakanin mabiya kowane addini da kabila, ”in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: