Kwamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba hatsi na kimanin miliyan bakwai

Kwamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba hatsi na Kusan naira Miliyan bakwai a gundumomin Kaugama da Marke da Dakkayawa dukkanin su dake karamar hukumar Kaugama ta Jihar Jigawa.

Kamar yadda rahotanni suka ruwaito, kwamitin ya raba buhun gero saba’in da takwas da buhun dawa dari da bakwai da buhun gyada uku gami da buhun wake goma da kuɗin su ya kai naira miliyan biyu da dubu dari bakwai kasar Kaugama kawai.

Har wa yau kwamitin ya raba makamantan hatsin a Kasar Marke da suka hada da buhun gyada saba’in da bakwai da buhun gero 157 da kuma dawa kudaden su ya kai naira miliyan daya da dubu dari.

Kazalika haka al’amarin yake a Kasar Dakkayawa inda aka raba buhun gero chasa’in da tara da buhun gyada da na dawa 312 da kudin su ya kai naira miliyan biyu sa dubu dari uku.

Da yake jawabi yayin rabon kayayyakin, Mataimakin Shugaban Kwamitin Zakkar wanda har wa yau shine Limamin babban Masallaci na Hadejia Sheikh Yusuf AbdulRahman ya ce baya ga zaman zakka daya daga cikin shika-shikan musulunci, kazalika tana kuma tsarkake dukiya daga fadawa bala’i.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, wani Shehin Mallami Dakta Umar Nassarawa ya jaddada cewa ita zakka fa wajibi ne kan duk wani musulmi da dukiyar sa ta kai ta zakkar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.