Zamba: karkatar da kudaden jama’a, halatta kudaden haram, EFCC ta sake gayyatar AbdulAziz Yari

 

Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnar jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya bayyana gabanta ranar Alhamis domin amsa wasu tambayoyi.

Hukumar ta umarci Yari ya bayyana a ofishunta dake Sokoto domin amsa tambayoyi.

Idan ba a manta hukumar ta gayyaci tsohon gwamnan a watan Faburairu ofishinta dake Legas, inda ya bayyana ya shafe awowi ya na amsa tambayoyi.

Ko a wancan lokacin an bukaci Yari ya amsa tambayoyin kokarin canja wa wasu biliyoyin naira wuri dake dankare a wani asusun bankin kasar nan.

Hukumar ta tsare Yari na wani lokaci mai tsawon gaske a Legas yana yi mata bayani akan wannan kudade har biliyan 300 da yake kokarin canja musu wurin zama daga wani bankin Najeriya.

Sai dai majiyar ta shaida mana cewa, bayan Yari ya kammala amsa tambayoyi daga jami’an hukumar EFCC sun umarce shi ya tafi, amma kuma idan ana bukatar wasu bayanan zai ga sammaci.

Wannan tuhuma ya zo kwanaki kadan bayan gwamnati ta kwace wasu kudaden tsohon gwamnan, wanda suka tabbata na shi ne amma kuma ya kasa bayyana gaban kotu yayi mata bayanin yadda ya same su.

Kudaden da ke jibge a wasu asusun bankuna daban daban na kwance ya kasa bayyana a kotu ya fadi yadda ya same su. Ganin haka kotu ta ce tunda mai kudin ya ki bayyana ya bada hujjojin mallakar kudaden ta yanke hukuncin a kwashe su kaf a maida asusun gwamnati.

An kwace masa dalar Amurka 56,056.75 a asusun Polaris Bank, sai kuma naira milyan 12.9 da kuma wasu naira milyan 11.2.

Akwai kuma wasu zunzurutun dalolin Amurka da aka ajiye har dala 301,319.99 wadanda su ma kotu ta kwace.

Sannan an kwace naira 217,388.04, sai kuma wasu dala 311,872.15 da ya boye a Zenith Bank, wadanda su ma kotun ta kwace daga hannun sa.

Premium Times

Leave a Reply

Your email address will not be published.