Muhuyi bai cancanci shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ba ~ Wata Kungiya

Wata kungiya da abin ya shafa ta kalubalanci halaccin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ci gaba da kasancewa a matsayin Shugaban Hukumar Korafi da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC)

Kungiyar mai suna “NASARAR GIDAN SARKI” ta bayyana cewa a bisa dokar jihar Kano da dokar hana cin hanci da rashawa ta 2008, babban ma’aikacin gwamnati ne kawai wanda ke da mutunci kuma za a iya amincewa da shi, Har a nada shi a matsayin Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kuma wannan aiki ne wanda ya keɓanta ga Majalisar Dokokin Jiha kawai.

Kungiyar ta kuma yi kakkausar tambaya kan ko Muhuyi ya taba yin aiki a matsayin ma’aikacin gwamnati, Don haka, suna neman ya fadawa jama’a sunan ma’aikatar da ya yi ritaya kafin wannan matsayin.

“A wana lokaci aka nada ka, har ka bayyana a gaban Majalisar Dokoki ta Jiha don tantancewa? Idan an tantance ka, yaushe hakan ta faru? “, Shugaban kungiyar ya ke tambaya.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa akwai karya dokokin hukumar da ta ba Muhuyi damar zama shugaban kungiyar.

Don haka, suka yi kira ga ‘yan ƙasa da su taimaka musu wajen samun amsoshin waɗannan tambayoyin, yayin da suka dage cewa idan Muhuyi ba zai iya bayar da amsoshin ba, to mutuncinsa abin tambaya ne.

Idan za a tuna, a kwanakin baya ne Muhuyi ya fara binciken mai martaba Sarkin Kano na yanzu, Alh Aminu Ado Bayero, kan batun sayar da filaye a Gandun Sarki, Dorayi Karama, da ke karamar Hukumar Gwale ta jihar.

Wani rahoto da hukumar wacce Muhuyi ke shugabanta, ta tuhumi sarkin a badakalar cinikin kasa, inda aka sayar wa da wani Yusuf Shuaibu Aliyu mai kadada 8 a kan N575m (a gidan Alhaji Ado Bayero Estate), da kuma hekta 14 a kan kudi N200m .

Kwamared Kabiru Saidu Dakata, wani fitaccen mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a jihar, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ya ce, “Muna kallo kuma mun zuba ido don ganin ko Muhuyi Magaji zai rubuta wa gwamnan tare da bayar da shawarar dakatar da Alhaji Aminu Ado Bayero ne ko kuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.