Daga Randa Mulki ya bar hannun ka to ka zama shashasha: Cewar Jonathan

 

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa mutane da dama na shafe shafin mutum da zarar madafun iko ya bar hannunsa.

 

Jawabin nashi na zuwa ne yayin da Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya gayyace shi kaddamar da ayyuka a Jihar, inda ya ce wasu mutane na nuna biyayyar su ce kurum lokacinn da suka ga ragamar komai a hannun ka.

 

“Akwai wasu mutane dake nuna tamkar ba za su iya cin abinci ba idan ba kai yayin da kake kan wani madafun iko, amma da zarar sun ga ya bar hannun ka sai ka ga suna nuna kamar ba a taɓa yin ka a rayuwa ba”

 

“Wannan rana ta yau rana ce ta farin ciki a gare ni, Kun san dalili? Saboda ba abu ne mai sauki ka yi aiki da wani a Najeriya sannan ya ci gaba da tunawa da kai bayan kun bar matsayin da kuke ba.

 

“Na kasance a madafun iko daban daban, farawa daga mataimakin gwamna”

“Darasin da nake gani shine, duk lokacin da ka yi bankwana da ofishin ka to daga ranar kun yi hannun riga da wasu mutane kenan” a cewar tsohon shugaban kasar.

 

Daga bisani Jonathan ya jinjina wa al’ummar Jihar Bauchi bisa yadda suka jajirce wajen kawo Bala Muhammad Kan karagar Mulki tare da nuna jin dadin sa kan yadda ya sauya Alkiblar jihar cikin kankanin lokaci.

 

Idan za a iya tunawa dai Sanata Bala Muhammad ya kasance Ministan Birnin Tarayya Abuja sa’in da Jonathan ke shugabantar Kasar na.

Leave a Reply

Your email address will not be published.