Babu Dalilin Da Zai Sanya In Koma Jam’iyyar APC ~ Matawallen Maradun

 

 

Gwamnan Zamfara Bello Mohammed Matawalle, ya musanta raɗeraɗin da ake yaɗa wa, na cewa zai bar jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC.

 

Wata sanarwa da Babban Daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Gwamnan, Yusuf Idris Gusau ya fitar a ranar Talata, ta ce Matawalle ya bayyana masu yaɗa wannan ƙar da ƙanzon kuregen a matsayin “haɗamammun ƴan siyasa masu neman suna”.

 

Sanarwar ta ambato Matawalle na cewa “Ban taɓa maganar koma wa APC da wani ɗan siyasa a matakin jiha ko ƙasa ba, babban abun da na saka a gaba yanzu shine, dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara, wanda ya gagara a lokacin mulkin APC a jihar”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *