Dubun Barawon Yara Daga Mararrabar Gurku Jihar Nasarawa Ta Ciki, Bayan Satar Dan Makocin Su

Mazauna Unguwar Albarka dake Mararrabar Gurku karamar hukumar Karu Jihar Nasarawa na ci gaba da Zama Cikin Zullumi da fargabar yadda ake yawan Satar Yara Kana a Unguwar, dubun wani matashi Mai suna Umar Wanda akafi sanin Mahaifin sa da suna Ustaz ta cika ne bayan samun sa da laifin Satar wani yaron makotan su Kuma ya sayar da shi Naira Dubu Daribiyar ga wani Mai Suna Bawa J. Madawaki dake zaune a Masaka River Site, Magidancin Mai Suna Bawa dai ana zargin sa da kafa gidan Marayu yana fakewa da safarar Yara.

Lokacin da jami’an tsaro Suka Isa Gidan sun tarar da Yara Biyar har da yaron da aka Sato daga Maraba Kuma har an sauya masa suna zuwa John, iyayen yaron sun bayyanawa wakilin mu cewa sun shafe kwana 25 suna Nan Dan nasu, Kuma sun yi murna da ganin shi.

Shugaban kwamitin Tsaro na Unguwar Albarka Maraba, Muhammad Bulama, yace ba wannan ne karo na farko da aka samu Umar da Satar Yara ba a yankin Dan haka, suna Kira ga Mai girma Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi A Sule da yasa ‘yan Majalisar Jiha su yi Doka duk gidan da aka samu Haka a rushe shi zuwa fili mallakin Gwamnati, ya yi Kira ga Jamar yankin da Hukumomi da Masu Unguwanni da su rika lura da Aiyyukan gidajen Marayu da ake budewa a yankin tare da Kai rahoton duk wani Abu da Basu fahimta ba.

Tambari

Leave a Reply

Your email address will not be published.