Buhari Bai Taba Alkawarin Daidai ta Dala Ɗaya ta koma Naira Ɗaya Ba – Femi Adesina

Buhari Bai Taba Alkawarin Daidai ta Dala Ɗaya ta koma Naira Ɗaya Ba — Femi Adesina

 

Fadar Shugaban kasa ta ce babu wani lokacin da gwamnati mai ci ta yi alkawarin sanya Naira daya ta zama daidai da dala daya.

 

Mista Femi Adesina, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya ce ikirarin da ke nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi irin wannan alkawarin, karya ne.

 

“Babu shi, karya ne, ƙirƙirar sa aka yi, babu shi” Mista Adesina ya faɗi haka ne a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a wani Shirin Siyasa Da wani Gidan Talabijin ya gayyace shi A Jiya Lahadi.

 

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published.