Dole Ne Mu Taimakawa Gwamnatin Buhari, Cewar Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na bukatar taimako, Daily Trust ta ruwaito.

Aiku Abubakar ya bayyana haka ne a cikin wata makala mai taken: ‘Matsakaicin rashin aikin yi mafi girma a Duniya: Lokaci Don Taimakawa Wannan Gwamnati ta Taimakawa Najeriya’.

Tsohon mataimakin shugaban kasar kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 ya bayyana cewa, taimakawa wannan gwamnati mai ci shine mataki na ceton ilahirin ‘yan Najeriya.

Ya ce maimakon sauraran shawarwari, gwamnatin tana karantar ma’anoni marasa kyau ga ra’ayoyi da shawarwarin da masu sukarta ke bayarwa.

Atiku ya kuma danganta yawaitar aikata laifuka da rashin aikin yi da kasar ke fuskanta wanda ba a taba gani ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.