‘Yan Yakin Kafa Biyafara Da Jamhuriyar Oduduwa Ba Su Da Bambanci Da Boko Haram, Inji Gumi

Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce masu neman kafa kasar Biafra da Oduduwa ba su da bambanci da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

 

Gumi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Pidgin a ranar Asabar yayin da yake magana kan halin rashin tsaro a kasar.

Malamin ya ce wannna ba adalci ba ne a ce ‘yan Nijeriya suna son a raba kasar saboda ayyukan wasu ‘bata gari’ wadanda kawai ke ingiza mugayen akidu da bukatunsu.

Malamin ya yi ikirarin cewa yawancin ‘yan Nijeriya suna son dunkulalliyar kasa inda zaman lafiya da daidaito zai yawaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published.