PDP Ta Kalubalanci Gwamnatin APC A Kano Kan Siyasantar Da Aikin Gwamnati

Shugabacin jam’iyyar PDP ta jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Shehu Wada Sagagi ta nuna rashin amincewarta da natakinda Gwamnatin APC karkashin Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje keyin barazanar xauka akan ma’aikatan Gwamnati muddin basuje sun karbi katin shaidar zama xan jam’iyyar APC ba kamar yanda shugaban rikon jam’iyyar ya faxa a kwanakin baya.

Yace su a matsayinsu na PDP suna kyamatar wannan mataki da nuna kinta ga wannan kalamai duba da cewa hakkin kowane xan jihar Kano ne ya zabi jam’iyyarda yakeso.

Alhaji Shehu Wada Sagagi yaja hankalin Gwamnatin Kano akan kasa ta cigaba da razanar da tsoratarda ma’aikatan Gwamnati a kyalesu ma suji da abinda sukeji na yanke musu albashi da ake na bakai ba gindi.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Kano yayi kira ga Kungiyar Kwadago akan kada tayi shiru akan wannan abu magana suna ganin kamar wasane,wannan yunkurine na wannan Gwamnatin ta Ganduje na siyasantarda aikin Gwamnati wanda hakan hatsarine ga al’umma da jihar Kano da kasa baki xaya.

 

Alhaji Shehu Wada Sagagi yayi kira ga dukkanin.ma’aikata su kwantarda hankalinsu babu zancen ace an razanasu an tsoratasu akan suyi rijista da jam’iyyar da basaso kuma ba abin.mamaki bane ganin yanda Gwamnatin.APC ta jefa al’umar Kano a talauci da fatara da yake damun mutane ya nuna karara cewa al’ummar Kano basa goyon bayan wannan jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *