Kisan Ƴar Aiki: Bayan kiraye-kiraye ƴan sanda sun saki hoton wadda ake zargi

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta saki hoton matar da ake zargi da yin ajalin ƴar aikinta.

 

Mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya fitar da hoton ta shafinsa na Facebook da misalin ƙarfe 1:50 na ranar Lahadi.

Wannan dai ya biyo bayan kiraye-kirayen da al’umma suka riƙa yi a kafafen sada zumunta kan ‘yan sanda su fitar da hotonta kamar yadda suke fitar da na waɗanda ake zargi da aikata laifuka.

 

Kiyawa ya ce, sun gurfanar da Fatima Hamza mai shekaru 30 a gaban kotu majistiri mai lamba da ke Gyaɗi-gyaɗi a Kano bisa zargin kisan kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.