Dattawan Arewa Sun Caccaki Masu Ruwa Da Tsaki Kan Yin Biris Da Laifukan Makiyaya

Gamayyar Dattawan Arewa Kan Zaman Lafiya da Cigaba sun yi kira ga masu ruwa da tsaki a yankin masu butulci kan abin da suka bayyana a matsayin nuna halin-ko-in kula dangane da shiru da suka yi kan fuskantar miyagun laifuka da makiyaya ke yi a duk fadin kasar ta yadda hakan zai bata sunan yankin.

Dattawan sun bayyana cewa dole ne yankin ya fara tofin Allah tsine kan wasu makiyaya masu aikata laifi idan har za a dauki yankin da muhimmanci. Sun ce Fulani makiyaya suna ci gaba da kasancewa masu yin amfani da dabara da kuma shirya ayyuka wajen aiwatar da manyan laifuka a duk fadin Nijeriya. Dattawan sun yaba da matakan da wasu malamai suka dauka, gami da bayar da misali da mashahurin Malamin addinin Islama kuma mai wa’azi, Sheik Abubakar Gumi saboda daukar kwararan matakai da nufin kawo karshen matsalar ta hanyar tattaunawa da ‘yan bindiga.

Gumi ya gana da wasu ‘yan bindiga a Zamfara a cikin mako guda da nufin kawo karshen ta’addanci a yankin. A cikin wata sanarwa daga Babban Kodinetan hadakar, Injiya Zana Goni, dattawan sun bayyana a matsayin “makircin abin kunya da babbar murya daga wasu sanannun dattawan Arewa da masu ruwa da tsaki wadanda ya kamata su tashi tsaye don yin magana game da munanan ayyukan.”

Sanarwar ta ce: “Mun damu matuka game da almubazzaranci da ayyukan aikata laifi na wasu daga cikin danginmu Fulani da kuma abin kunya da babban makircin yin shiru da wasu fitattun dattawanmu na Arewa da masu ruwa da tsaki wadanda ya kamata su tashi tsaye don yin magana kan munanan ayyukan.

 

“Wadannan munanan dabi’un da wasu ‘yan uwan mu suke yi wadanda suke nuna kansu a matsayin makiyaya abin aibu ne sosai kuma dole ne mu fara magana akan su yanzu idan har za a dauke mu da mahimmanci a Nijeriya. “Ayyukan wasu daga cikin wadannan makiyayan masu laifi sun fara ne kamar wasa kuma saboda mun yi shiru wanda ya nuna cewa mun fi su goyan baya, sai suka tsaurara ayyukansu wadanda suka yi nadama suka same mu a wannan halin da muke ciki.

 

“Duk da cewa dole ne mu yarda cewa su na iya kasancewa wasu masu hadin gwiwa na cikin gida, Fulanin sun kasance jagorori da a cikin galibin ayyukan aikata laifuka da ke gudana a fadin kasar a yau. Wannan bai kamata ya zama abin karbuwa a cikinmu ba, kuma dole ne a dakatar da shi yanzu.

 

“Gangar yakin da ba ta da lafiya da ke ci gaba da tabarbarewa a halin yanzu a Nijeriya a yau ta samo asali ne sakamakon rashin tsaro da ayyukan wadannan ‘yan uwa namu, kuma hakan sai aka samu wasu daga cikin manyanmu suka ci gaba da yin shiru gami da ci gaba da sa ido suna kallon lamarin yana yaduwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *