Siyasar Zamfara : Za’a dinke baraka a jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC mai adawa a jihar Zamfara wadda ta daɗe tana fama da rikicin cikin gida, lamarin da ya kai ga rasa kujerar Gwamna a zaben shekarar 2019, ta fara zaman sasanci da jiga-jigan jam’iyyar.

 

A baya dai Jam’iyyar ta rabu gida biyu, ɓangaren tsohon Gwamnan jihar Abdul-aziz Yari da kuma ɓangaren Sanata Kabir Garba Marafa.

 

Sai dai a yanzu Jam’iyyar za ta dunƙule wuri guda, a dai-dai lokacin da aka fara sabunta rigistar mambobin Jam’iyyar kamar yadda Sanata Marafa ya shaidawa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba a wata tattaunawa da ya yi da shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *