Saboda Ban Goyi Bayan Ganduje a Zaɓen 2019 ba Ya hana Ni Wa’azi – Nasiru Kabara

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Malamin addinin musulunci a Kano da gwamnati ta dakatar daga yin wa’azi ya soki gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa hana shi wa’azi don bai goyi bayan gwamnan a zaben shekarar 2019 ba.

 

Yayin da yake zantawa da jaridar Daily Trust jim kadan bayan umarnin da gwamnatin Kano tayi na dakatar da shi, malamin ya ce anyi hakan ne saboda siyasa ba wai don addini ba.

 

“Dalilan a bayyane suke. Mutumin da ya dau wannan matakin(Ganduje) ya sha fadi sau da yawa cewa bazai taba yin yafiya ba. Na yake shi a zaben da ya wuce kuma yayi alkawarin zai rama. Kawai dai yayi hakan ne a lokacin da bai dace ba. Wannan dakatarwar siyasa ce, ba tada alaka da addini ko samar da tsaro.

 

“Na fadawa magoya bayana da su shirya kuri’unsu a zaben gaba kuma suyi abinda yakamata. Nagode Allah kan komai, ina rigima ne da malamai ba gwamnati ba, sai dai gwammati ta shiga cikin fadan amadadinsu.

 

” wannan ya nuna cewa basu da amsar dukkan tambayoyina. Tayaya gwamnati tasan cewa ina ingiza mutane su tada rikici? Shin suna karanta litattafan da nake kafa hujja dasu kafin nazo na dau matsaya? Shin suna ma da ilimi a kan su?.

 

“Yakamata ace sun binciki litattfan da nake kafa hujja da su amma basu yi haka ba sai dai suka yi rashin adalci gareni.”

 

Malamin ya bukaci mabiyansa da suyi hakuri su kuma ci gaba da addu’a.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.