‘Kowanne Ɗan Ƙasa Yana da Ƴancin Rayuwa a Duk Inda yake so’, El-Rufai ya yi Allah-Wadai da Korar Fulani

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya yi Allah-Wadai da “Korar Fulani ba bisa ka’ida ba” da ake yi a fadin kasarnan, inda yayi bayanin cewa, kowanne dan kasa yana da hakkin zabar inda zai zauna.

 

Bayanin nasa na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake kiraye-kirayen Fulani Makiyaya da su bar yankin kudancin Najeriya bisa matsalar tsaro da ake fuskanta.

 

“Amadadin gwamnatin jihar Kaduna, ina kira ga dukkan Yan Najeriya da suke zaune a jiharmu da su girmama doka da Oda da kuma hakkin dukkan yan kasa na yin rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya a duk inda suke zama ko suke aiki. Ina kira ga yan uwana gwamnonin jihohi da su yi irin wannan bayanin, tare da dakile wadannan hare-hare”, inji gwamnan.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.