Korona: Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Taruka, Ta Umarci Ma’aikata Su Yi Zaman Gida

Gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin sake kafa dokar rufe gidajen kallo da wuraren tarukan bukukuwa a fadin jihar Kano sakamakon sake bullar annobar Korona. Kwamishinan ma’aikatar yada labaran Jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa day a fitar da safiyar Talata.

 

Malam Muhammad Garba yace wannan mataki shi ne matsayar masu ruwa da tsaki da suka dauka a lokacin taron da aka gudanar ranar litinin a fadar Gwamnatin Jihar Kano, yace dukkan ma’aikatan Gwamnati an umarce su das u zauna a gidajensu har zuwa lokacin dasu ji wani umarnin.

Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa, sauran masu ayyuka na musamman irin jami’an lafiya, jami’an kasha gobara, hukumar bada ruwan sha, malaman makaranta, jami’an tsari da ‘yan Jaridu basu cikin wadanda wannan rufewa ta shafa.

Daga nan sai Malam Muhammad Garba ya kara jadadda aniyar Gwamnatin Kano na kara jajircewa wwajen yin aiki da dukkanin masu ruwa da tsaki wadanda suka hada da malaman addini domin tabbatar da yin aiki da dukkanin matakan kariya daga annobar Korona.

Daga nan ya bukaci jami’an tsaro wadanda ke cikin rukunin masu ruwa da tsaki dake cikin taron da aka gudana ba zasu yi kasa a guiwa ba wajen daukar dukkan matakin da ya kamata domin tabbatar da ganin ana kiyaye matakan kariya da aka gindaya.

 

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano cewar ko Gwamnatin Kano na niyyar sake rufe gari ne baki daya, sai Malam Muhammad Garba yace, kamar yadda aka sani an gudanar da taron da masu ruwa da tsaki kan lamarin annobar ta Korona wadda ahalin ke kara yaduwa a a karo na biyu, yace kowa yaji irin umarnin da shugaban kwamitin karta kwana na Gwamnatin Tarayya Boss Moustapha wanda ya koka kan yadda ake samun yawaitar yaduwar wannan cuta, wanda hakan ke nuni da cewa matukar aka ki bin umarnin kwamitin karta kwana, kila dole takai ga sake rufe gari kamar yadda akayi a karon farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published.