Boko Haram Ta Rasa Inda Za Ta Saka Kanta A Borno – NAF

Rundunar Sojin saman Nijeriya NAF, bangaren dakarun ‘Operation LAFIYA DOLE’ ta rusa wani sansanin horar da ‘yan ta’addan Boko Haram, tare da wani da ake zargin cewa an ajiye makamai, sannan kuma rundunar ta kashe ‘yan ta’addan da dama a Nuwar da ke yankin Bama na jihar Borno.

 

Jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ne bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu cikin makon nan, a inda yake cewa, an aiwatar da hakan ne ta hanyar kai hare-hare ta sama da aka zartar a ranar 14 ga Janairun 2021, biyo bayan rahotannin sirri da ke nuna cewa rukunin gidaje da sauran gine-ginen da ke wurin ana yin amfani da su don gudanar da horon yaki ga ‘yan ta’addan akai-akai.

A sakamakon haka ne, bayan rundunar ta gudanar da wasu jerin ayyukan sa ido a sararin samaniya, sai ta aika da rundunar da ta dace da jiragen yaki masu saukar ungulu na rundunar Sojan Sama (NAF) don kai farmaki ta dare a wurin.

Jiragen sama masu saukar ungulu sun yi mummunar illa a yankin da aka hara, wanda ya haifar da sanadin salwantar rayukan yawancin ‘yan ta’addan tare da lalata wasu gine-ginensu, gami da ma’ajiyar makaman su, inda aka gano suna ajiye kananan abubuwan fashe-fashe da yawa a cikin. An kawar da wasu ‘yan ta’adda da dama a ci gaba da kai hare-hare ta jiragen yaki masu saukar ungulu.

A wata sanarwar kuma, John Enenche ya bayyana cewa, bayan nasarar dakile harin da ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan kungiyar ISWAP ke shirin kai wa garin Marte, tare da lalata manyan motocin bindigoginsu 7 ta hanyar zartar da harin hadin gwiwa tsakanin sojin kasa da na sama, Rundunar Sojin Sama NAF, bagaren dakarun ‘Operation LAFIYA DOLE’ ta murkushe wasu manyan motocin daukar bindiga 6, tare da kawar da dimbin ‘yan ta’addan da ke kokarin karfafa abokan aikinsu a hari ga al’umma.

 

Wannan ya faru ne a daren 15 ga Janairun har zuwa wayewar garin 16 ga Janairun 2021, yayin da jiragen sama masu saukar ungulu na rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) suka yi wa jerin gwanon motocin daukar bindigogi na ISWAP kawanya, yayin da suka kusanci layin Marte don kai hari.

 

Jirage masu saukar ungulu sun yi lugudan wuta akan ‘yan ta’addan a hare-hare, tare da kawar da karancin motocin bindigogi 6, wadanda aka gani suna cin wuta a cikin filin daga. Wasu ‘yan ta’adda da yawa sun kasance cikin shirin kai hare-hare yayin da jiragen yaki masu saukar ungulu ke ci gaba da tarwatsa ‘yan kungiyar ISWAP da ke guduwa.

 

Sojojin Nijeriya, suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki, za su ci gaba da kai hare-hare a kan makiyan babbar kasarmu.

Suka ce, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai an samu zaman lafiya da daidaito ba kawai a Arewa maso Gabas ba, aa har ma da duk wani yanki mai fama da rikici na kasar mu abin kauna.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *