Annobar Sace Farfesoshi Ta Kunno Kai A Arewa

An Sace Farfesa, An Kashe Dansa Da Mutum Uku A Kaduna

An Sace Wani Farfesan A Nasarawa

 

 

Daga dukkan alamu annobar sacewa tare da yin garkuwa da shehinnan jami’a ya fara kunno kai a Arewa, inda lokaci-lokaci akan bayar da rahotannin sacewa, bindigewa ko yin garkuwa da su, inda akan kai hari har gidajensu.

A jiya ne wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka sace farfesan kimiyyar da lissafi a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma, ta Jihar Katsina a kan babbar hanyar Akwanga zuwa Keffi. Farfesa Johnson Fatokun wanda ke tuka mota daga Jos ya nufi Keffi da misalin karfe 9:00 safiyar ranar Talata wasu gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka yi masa kwanton bauna. Wani da ya tsira wanda ya yi magana da manema labarai a Lafi ya ce yayin da suke tunkarar Garaku a Karamar Hukumar Kokona ta jihar, wasu mutane sun fara harbin kan mai uwa da wabi a bayansu.

Farfesan da ke tuki ya yanke shawarar kara sauri, ashe yana kara shiga cikinsu ne, kawai bai aune bas ai y aga wasu gungun ‘yan fashi a gabansa, suka daka musu tsawa,suka tsayar da su. “ A lokacin da muka tsaya, sai suka umarce mu shiga cikin daji kuma suka fara magana da yaren Hausa, a lokacin da na fada wa daya daga cikinsu cewa bana jin Hausa, sai ya sa bindiga yana kokarin harbe ni, sai ya gano babu harsashi, ” a cewar wanda ya tsira.

Ya ci gaba da bayanin cewa lokacin da ya gano babu harsashi a cikin bindiga, sai ya fito da wata wuka mai kaifi yana so ya soka masa amma da kyar ya kubuta daga gare shi ya boye kansa a cikin magudanar ruwa. Yayin da ‘yan bindigan suka ci gaba da nemansa, wanda ya tsira ya ce an sanar da tawagar sojoji kuma sun zo sun yi artabu da masu laifin yayin da ‘yan kungiyar masu dauke da makamai suka gudu zuwa daji tare da farfesan.

 

Ya ce wasu daga cikin masu garkuwan sun sanya kayan ‘yan sanda kuma suna da cikakkun makamai. Ya kuma bayyana cewa ya ba da bayani a ofishin ‘yan sanda na Garaku inda ya ce motar farfesan an same ta da ramukan alamar harbin harsashi a ajiye a halin yanzu. Masu garkuwan suna neman a basu Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa kafin a sako farfesan.

 

A wata annobar labarin ma, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne, sun sace wani basaraken gargajiya, Wazirin Wusasa, Farfesa Aliyu Mohammed, a gidansa da ke unguwar Wusasa a Zariya tare da kashe dansa, Abdulaziz Aliyu, yayin samamen. Sun kuma kashe wani mutum a wasu hare-hare daban-daban da aka kai a kauyen Anaba da garin Birnin Yero, duk a cikin Karamar Hukumar Igabi.

 

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindiga a wasu hare-hare daban-daban sun kai hari kan Kananan Hukumomi uku da ke Kaduna a ranar Lahadi, inda suka kashe mutane hudu, ciki har da wani Farfesa da dansa, ‘yan banga biyu da wani mutum daya.

Kwamishinan ya bayyana sunan wanda aka kashe a Igabi wani mutum ne Lawali Abdulhameed, wanda aka harbe a kokarin tserewa. A cewarsa, ‘yan bindiga sun afka wa Wusasa a Karamar Hukumar Zariya inda suka yi garkuwa da Wazirin Wusasa (mai rike da mukamin), Farfesa Aliyu Mohammed, a gidansa yayin da aka kashe dansa, Abdul’aziz Aliyu a yayin harin.

 

Ya kuma kara da cewa, dan gidan Farfesa, wani Abba Kabiru, wanda ke cikin gida lokacin da lamarin ya faru an harbe shi kuma ya ji rauni.

 

A cewar kwamishinan, wasu’yan fashin kan babura da yawa sun afkawa kauyen Iyatawa na Karamar Hukumar Giwa, amma wasu ‘yan banga suka fatattake su, suka tilasta su tsere.

 

Ko ma dai yaya, Aruwan ya lura da biyu daga cikin ‘yan banga da suka yi artabu da ‘yan ta’addan, “Biyu daga cikin ‘yan banga na yankin, Malam Auwalu da Alassan Shehu, sun mutu yayin arangamar lokacin da aka hanzarta kai komo na sintiri zuwa wurin don gudanar da aikin gama gari.

“Gwamna Nasir El-Rufai lokacin da ya karbi rahotannin, ya aike da ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe da kuma ‘yan banga, inda ya yi addu’ar Allah Ya jikan su. Ya kuma yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

 

“Gwamnan ya kuma yi godiya ga sojoji kan hanzarin da suka yi wajen tura dakaru zuwa yankin da abin ya shafa a Karamar Hukumar Giwa. Ya kara da cewa Kungiyoyin ‘yan banga a yankin sun tunkari ‘yan fashin, a karshe suka tilasta musu tarwatsawa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *