‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane Sha Takwas Tare Da Kashe Mutum Biyu A Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

A daren jiya Juma’a Ne, ‘yan bindiga suka kai hare-haren a kauyukan kananan hukumomi Batsari da Faskari da kuma Sabuwa a jihar Katsina, inda suka sace mutane goma sha takwas da kashe Mutum biyu a Batsari har lahira.

Majiyar RARIYA ta tabbatar mata cewa a daren jiya, sun zo bisa mashina,dauke da bindigogi, suka je garin Daurawa (Garin Ajiya), da ke cikin karamar hukumar Batsari, inda suka kashe mutane biyu kuma suka sace mutum biyu. Sun je garin Kasai da ke karamar hukumar Batsari, sun sace Mata ukku, yanzu haka suna hannun su.

Haka zalika, duk dai a daren jiya, ‘yan bindiga sun kai makamancin wannan hari a garin Albasun Liman Sharehu, da ke gundumar Gamji a karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina, inda suka je garin da misalin karfe sha daya da rabi na daren jiya Juma’a, suka Sace mutane takwas, matan aure ukku da kuma matasa biyar.

Duk dai a daren jiya, Majiyar RARIYA ta shaida Mata cew ‘yan bindiga, Wanda yawansu sun kai talatin, kuma a kasa suka shigo garin, dauke da bindigogi, sun kai hari a garin Unguwar Sakkai, da ke cikin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, inda suka sace mutane biyar, akwai Amadu Dansidi da Sanaya da Naja’atu da Zaliha da Sadiq. Amma ba su kashe kowa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.