Fulani ne dake tsakanin Dajin Zamfara da Katsina suka sace Dalubai yan Makarantar Kankara ba Boko Haram ba – Inji Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun ya ƙaryata Shugaban Ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau inda ya ce Sam ba ‘yan Boko Haram ba ne suka ɗauki Yara ɗaliban Kankara, inda yace wasu Filani ne ‘yan Ta’adda dake tsakanin Katsina da Zamfara suka sace su, kuma a Hannun su suka karɓo su a wani Daji dake Jahar Zamfara.

Bello Mutawalle yace da Shugaban Miyetti Allah na Kasa da wasu jami’ai suka shiga Dajin da Misalin Karfe 6, akan bukatar ayi sulhu tare da sako yaran, wanda hakan ya sanya aka saki yaran.

Gwamnan ya kara dacewa, har Mataimakin Shugaban Kasa ya kira shi akan Gwamnatin tayi duk yadda zatayi domin sako su, inda Gwamnatin ta nemi wasu Fulanin da suka yadda da ayi sulhu akan suje suyi zama da Barayin, don gani an kubutar da yaran, kuma sunyi zama har sau uku kafin su kira su bayarda Yaran.

Matawalle ya bayyana cewa basu bayarda ko sisi ko kuma musayar wani abu da nufin a sako yaran, Wanda an samu nasarar sako yaran ne, ta dalilin Sulhu da akayi da Barayin ta hannun Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa.

Gwamnan yace tuni suka hannanta Yaran ga Shugaban Soji Mai kula da Katsina da Zamfara da Sokoto Aminu Bande, kuma Gwamnatin Katsina ta turo motocin daukar su, kuma sun dade da isa Jahar Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published.