Sabon Shugaban ‘Yan Kasuwan Jihar Nasarawa Ya Bukaci Hadin Kai

Sabon Shugaban riko na yan kasuwan jihar Nasarawa Alhaji Turaki Gamji ya bukaci hadin kan ‘yan kasuwan. Shugaban ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya’yan kungiyar suka kira.

Alhaji Turaki Gamji ya ce da zuwan su kan kujerar Mulkin wannan kungiyar na watanni sun samarwa kungiyar da mazauni na ta da ya’yan shugabannin kungiyar za su rika zama suna tattaunawa.

Ya ce yanzu kungiyar tana da tsarin mulkin ta wanda ya baiwa kowani dan kasuwa dama da kuna hakin gudanar da kasuwanci.

Turaki Gamji ya ce hadin kai da zaman tare da gaskiya da rikon amana shi ne kadai zai kai kungiyar zuwa ga matakin nasara.

Ya bukaci mambobin kungiyar na ko ina a fadin jihar Nasarawa birni da karkara da su zama tsintsiya madaurin ki daya.

Cikin kasidar da aka karanta ya bayyana yadda jagorancin kungiyar zai gudana da matakan da za a dauka kan duk wanda ya sabawa kungiya ko ya yi almundahana da dukiyar kungiya ko makamancin haka a harkan kasuwanci.

kungiyar ta zargi tsohon Shugabanta Alhaji Shammasu Dan tsoho da yin rub da ciki kan miliyoyin nairori mallakin kungiyar.

Kuma ta bukaci ya dawo da wannan kudin ko kuma ta makashi gaban kuliya.

Alhaji Shammasu Dan tsoho shi ne tshon Shugaban kungiyar yan kasuwa ta jihar Nasarawa, membobin kungiyar sun zarge shi da wawushe dukiyar asusun ya’yan kungiyar ta karamar Hukumar Lafia.

Taron da ya gudana a zauren taro na Sandaji dake layin B Dibision a cikin garin Lafia ya samu halartan Shugabannin kungiyar daga wurare dabam dabam a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.