Ma’aikatan INEC Biyu Sun Yi Batan Dabo A Zaben Dan Majalisar Jihar Zamfara

Wasu ma’aikatan wucin-gadi biyu na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) sun yi batan dabo bayan zaben cike gurbin dan majalisar jiha mai wakilitar karamar hukumar Bakura a jiya Asabar.

 

A safiyar yau Lahadi, jami’in da ke tattara sakamakon zaben na INEC, Farfesa Ibrahim Magawata ya bayyana zaben cike gurbin na mazabar Bakura a matsayin wanda bai kammala ba.

Sannan kuma ya bayyana cewa, wasu Ma’aikatan Hukumar sun yi batan dabo ba a san inda suke ba.

Kawo yanzu, dan takarar jam’iyyar (PDP), Alhaji Ibrahim Tudu, yana kan gaba da yawan kuri’u 18,645, yayin da dan takarar APC, Alhaji Bello Dankande Gamji, ya samu kuri’u 16,464.

 

A cewar jami’in tattara sakamakon zaben na INEC, ya bayyana zaben a matsayin wanda ba a kammala ba sakamakon rikicin siyasa da ya barke a ‘Yargeda sannan kuma an siye kuri’a a mazabu takwas na garin Bakura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: