A Bauchi APC Ta Lashe Zaɓen Cike Gurbi

Babban Jamiyyar adawa ta APC a Jihar Bauchi ta lashe Zaben cike gurbi na dan Majalisar mazabar karamar hukumar Dass a Majalisar Dokokin Jihar.

Da yake bayyana sakamakon zaben, Baturen zaben Parfesa Ahmed Mohammed na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, ya bayyana dan takarar Jamiyyar APC Hon. Bala Lukshi a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 12,299 inda ya kada abokin takararsa na Jamiyya PDP mai mulkin Jihar, Alh. Lawal Wandi wanda ya samu kuri’u 11,062.

 

Baturen zaben yace “bayan cika dukkan ka’idojin dokan zabe, kuma da samun kuri’u mafi rinjaye a zaben, don haka Hon. Bala Lukshi na Jam’iyyar APC ya zama shine wanda ya lashe zaben”.

 

A wata majiya ta wayar tarho har ila yau, ta gaya ma labaran ‘Muryar Yanci’ cewa an bayyana sakamakon zaben cikin dar-dar da zullumi, inda tace Wakilan Jam’iyya mai mulki ta PDP suna ta hargowa, yayin sanar da sakamakon a offishin hukumar zabe na karamar hukumar Dass.

 

Majiyar tace “dole ala tilas muka sulale muka bar wajen a cikin daren don gudun abunda ka iya faruwa a sanadiyyar bayyana sakamakon zaben”.

 

Dama tun a farko rahotanni sunyi nuni da cewa, zaben zai zama yar manuniya, ko kuma zakaran gwajin dafi, tsakanin jigogi biyu a siyasar Jihar Bauchin, wato gwamna mai ci Sanata Bala Abdulkadir Mohammed da kuma tsohon kakakin majalisar tarayya Hon.Yakubu Dogara, wanda ya fito daga mazabar tarayya na Dass/ Bogoro da Tafawa Balewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.