‘Yan Bindiga Sun Yi Mummunan Ta’asa A Jihar Neja

Wasu ‘yan bindiga akan babura dauke da muggan makamai sun kai hari Unguwar Mai Jaki dake yankin Gunna na karamar hukumar Rafi a jihar Naija.

‘Yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 11, na safiyar yau Asabar inda suka sace shanu 100 mallakin Alhaji Garba, Musa Garba da Ado Garba.

 

Yayin da suka gama satar, akan hanyarsu ta komawa mabiyarsu, ‘yan Bindigar sun kuma lalata gidan shugaban kauyen, Malam Sallau Danladi Pangu da kuma Wani Asibiti da Bankin Duniya ya gina a kauyen, kamar yanda Majiyarmu ta bayyana.

 

Hare haren ‘yan bindiga na cigaba da ƙara ƙamari a yankin Arewacin Najeriya, inda dandazon ‘yan Bindiga akan Babura ke shiga ƙauyuka su lashe sa’o’i da dama suna barna ba tare da zuwan jami’an tsaro ba, sai bayan sun kammala da tsawon lokaci kafin jami’an tsaro su iso.

 

Halin da taɓarɓarewar tsaro ke fuskanta a yankin Arewacin Najeriya ya sanya ake ta kira ga shugaban ƙasa Buhari da ya yi gaggawa sauka daga mulki saboda ya gaza.

 

Sai dai a bangaren gwamnati ta bayyana wadannan kiraye kirayen da ake yi a matsayin siyasa maras tsafta, kuma haƙar masu wannan ɗabi’a ba za ta cimma ruwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.