Zaben Cike Gurbi: EFCC Sun Kama Hadimin Gwamnan Bauchi

Hukumar yaki da ta’annuti wa tattalin arziki (EFCC) ta cafke gami da tsare babban mai baiwa gwamnan Bauchi shawara kan lamuran ma’aikatan gwamnati, Mista Abdon Dalla Gin jim kadan bayan da ya kada kuri’ar a zaben cike gurbin dan majalisar dokokin jihar Bauchi ta mazabar Dass a Asabar din nan.

An cafke shi din ne bisa zarginsa da zuwa wurin zabe da kudade, inda ya shafe tsawon awanni biyar a caji ofis din ‘yan sanda da ke Dass daga bisani aka sake shi bisa beli. Wani ganau ya shaida mana cewa an cafke Gin ne a yayin da yake kokarin tuka motarsa gami da tafiya bayan da ya jefa kuri’ar, sai dai babu tabbacin an ga ya ciro kudin domin sayen kuri’u daga wajen masu zabe. Da ya ke zantawa da ‘yan jarida a yayin da lamuran suka yi kamari, Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Lawan Tanko Jimeta, ya shaida cewar sun ware jami’an ‘yan sanda sama da 600 da suka sanya ido domin tabbatar da zaben ya tafi cikin kwanciyar hankali.

Ya tabbatar da batun tsare hadimin tare da cewa suna kokarin samun cikakken bayani kan dalilin kamun da aka masa a daidai lokacin da aka zanta da shi.

Bayan da aka sake wanda aka kaman, Lauyansa Mukhtar Abubakar Othman, ya saida cewar EFCC ba su kama Gin na rabon kudi a yayin zabe ba, illa sun bude motarsa gami da kama kudin da bai kai miliyan da yaba a ciki. Ya shaida cewar a matsayin Gin na tsohon shugaban ma’aikatan jihar, yana da dama da zarafin yawo da adadin wannan kudin, “Kudi ne wanda ya ke da damar yawo da ita. Bai wuce dubu dari biyar ba,” Lauyan ya ce EFCC da ‘yan sanda suna da iko da damar tsare duk wanda suke zargi, amma babu kama Gin na rabon kudi ga masu zabe ba.

Duk kokarin da muka yi don jin ta bakin hukumar EFCC kan wannan batun hakan ya gagara.

Shi ma da ya ke bayani bayan jefa kuri’arsa Sarkin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Othman ya jinjina bisa yadda zaben ke tafiya bisa kwanciyar hankali, sai ya nemi jama’a da su kwantar da hankalinsu su bi komai a hankali.

An samu fito da kayan zaben a kan lokaci kamar yadda masu kada kuri’ar suka shaida, kana an samu fitowar masu kada kuri’a sosai.

Wakilinmu ya nakalto cewa zaben wanda ya fi zafi a tsakanin PDP da APC an fafata kada kuri’a ba tare da wani tashin hankali ba.

An samu gurbin kujerar ne dai bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe dan Majalisar da ke kan kujerar Hon. Musa Mante Baraza a watannin baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: