Gwamnan Zamfara Ya Zargi Ministan ‘Yan Sanda Da Yari Kan Kashe-kashe A Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle, ya zargi Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Alhaji Maigari Dingyadi, da tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari da daukar nauyin ‘yan bangar siyasa wadanda suka kaddamar da hare-hare ba kakkautawa kan mambobin jam’iyyar (PDP) a cikin karamar karamar hukumar Bakura. .

Harin da aka yi zargin ya haifar da mutuwar magoya bayan PDP biyu a yayin yakin neman zaben dan majalisar jiha na Bakura wanda za a duganar dashi gobe Asabar.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a daren Juma’a jim kadan bayan dawowarsa daga garin Bakura.

A cewarsa, abin da Yari da ministan harkokin ‘yan sanda suka yi wa jama’arsa ya saba wa tsarin dimokiradiyya da rashin sanin ya kamata.”

 

“Ina ganin Ministan harkokin‘ yan sanda kasancewarsa dan yan kin mu ne na Sakkwato, tun da ka hau, kujerar Minista bai taba yin wani abin da zai taimaka mana ba wajan kawo karshen matsalar tsaron da ta addabemu ba na rashin tsaro a Zamfara da jiharsa,amma abin takaici sai ya zo ya haifar da tashin hankali suna gaba da tankokin yaki gaba da baya sukai sanadiyar Kashe mutum biyi akai masu yankan rago a Bakura sabo da zaben dan majalisar jihar.

Akan haka ne Gwamna Matawalen ya yi kira ga shugaban kasa ya dauki mataki akan ministan da tsohon gwamna Yari Abubakar.

Gwamna Bello Matawalen Maradun, bukaci mambobin jam’iyyar PDP a jihar da su ci gaba da kasancewa ‘yan kasa masu bin doka da oda kuma su kasance jakadu na kwarai musamman yayin yakin neman zabe. da kuma ranar Asabar da za a gudanar da zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published.