Ana kace-nace kan matsayin ‘Farfesa’ ga Ganduje

 

 

Jami’ar East Carolina (ECU) da ke ƙasar Amurka ta musanta bai wa gwamnan Kano aikin koyarwa da kuma Farfesa.

 

Rahoton jaridar Premium Times ya rawaito jami’ar na cewa wasiƙar da wani ma’aikacinta ya aike wa gwamnan ba ta da amincewar hukumar jami’ar.

 

A ranar 1 ga watan Disamba ne sakataren yaɗa labaran gwamna Ganduje ya bada sanarwar cewa jami’ar ta naɗa gwamnan a matsayin Farfes tare da ba shi aikin koyarwa.

Sai dai sanarwar da jami’ar ta fitar a baya-bayan nan ta rushe wannan batu.

 

Freedom Radio ta tuntuɓi sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano sai dai ya ce ba a bashi iznin yin magana ba.

 

Al’umma na ta cecekuce a kai

 

Tuni al’umma suka shiga bayyana ra’ayoyinsu a kai, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun riƙa amfani da maɓallin Hash Tag da suka kira #VisitingFarfesaChallenge.

 

Ga wasu cikin masu yin tsokaci a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: