Tsaro Jihar Kaduna Ke Buƙata Ba Gasar Marathon Ba – Mr LA

Honorabul Lawal Adamu Usman wanda akafi sani da Mr LA ya bayyana matsalar garkuwa da mutane a matsayin abu mafi muni dake lalata tattalin arzikin kowace al’umma.

A halin da talakawan jihar Kaduna ke ciki na zaman dar dar da rashin madogara babu abinda gwamnati ya kamata ta maida hankali akai da ya wuce tsaro. Ko a safiyar yau an wayi gari a garin rigasa dake karamar hukumar igabi yan bindiga sun hallaka mutane tare da yin garkuwa da mutanen da ba suji ba su gani ba.

 

Ina kira ga gwamnatin jiha Kaduna da na tarayya da sa lalubo mafita game da matsalar garkuwa da mutanen nan tun kamin lamarin yazo yafi karfin kowa. Domin muddin ba a lalubo bakin zaren yanzu ba nan gaba matsalar zata wuce tunanin kowa.

 

Masu garkuwa da mutanen nan a waya suke magana da iyalan wanda suka sace,kuma wani abin ban dariya ma kanfanonin saddarwan nan suna samun kudin sadarwan su sakamakon katin kiran waya da ake zantawa tsakanin su Kuma duk da haka ace anrasa samun ingantattun bayanan da za ayi anfani dasu wurin kawo karshen matsalar wannan matsalar. Indai har gwamnati nason kawo karshen matsalar nan dole sai an sawa kanfanonin sadarwan nan wasu dokoki masu tsauri ta yadda za abasu lokaci kankani su bayyana masu anfani da layin ko kuma yadda za a same su cikin sauki ba tare da an dauki dogon lokaci ba. Idan har kanfanonin sadarwan suka kasa bada muhimman bayanai akan su toh ai masu tara mai yawa fiye da kudaden da za a biya masu garkuwa da mutanen,insha Allahu sai kaga anfara samun saukin matsalar.

 

Kuna ganin wannan shawarar da Mr LA ya bada zai iya kawo saukin matsalar garkuwa da mutane musamman jihohin mu na Arewa ?

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.