Yadda Kauraye Suka Sa Jama’a Gudun Famfalaki A Garin Mararraba/Nyaya Dake Abuja

FARGABAR ZANGA-ZANGAR RUSHE SARS

Daga Aliyu Ahmad

 

A yammcin yau ne jama’a suka yi ta gudun ceton rai a yankin Mararraba/Nyaya dake Abuja, biyo bayan zaman dar-dar da ake yi sakamakon zanga-zangar rushe SARS.

 

Saidai a yayin da RARIYA ta yi tattaki zuwa Mahadar Mararrba (Junction), ta nemi jin ta bakin wasu da ta ci karo da su a hanya.

 

“Gaskiyar abinda ya faru shine biki ake yi na wani Maidawa a unguwar Katsinawa, wanda hakan ya sa ‘yan uwansa kauraye suka dinga wasa da sanduna da wukake, inda bayan sun biyo kan titi suna wasan sai jama’a suka soma gudu, tunanin su ana rikici ne”, cewar wani mazaunin Mararraba, Aminu Bala.

Leave a Reply

Your email address will not be published.