Gwamna Abdulrazaq ya ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 24

 

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahaman Abdulrazaq, ya sanya dokar hana fita na sa’o’I 24 ga mutanen jihar daga tsakar daren yau (Asabar).

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani shirin da aka watsa a duk fadin jihar ta gidan Redion Midland 99.1 FM.

Abdulrazaq ya ce, “Ana yin barazana ga rayuka. Ana wawure harkokin kasuwanci. An yi niyya ga dukiyoyin jama’a. Wannan ba abin yarda bane. Ba kuma zamu amince ba.

“Don dakile wannan aika-aika na aikata laifuka, Ina sanar da dokar hana fita na sa’o’I 24 a cikin garin Ilorin daga tsakar daren jiya 23 ga Oktoba, 2020. Wannan ya yi daidai da Sashe na 1, 2 da 4 na Dokar Jama’a Kashi na 382 na Tarayyar Najeriya. 2004.

“An yi kira ga mutane da su kasance a cikin gida domin bin wannan dokar hana fita. Za’a sake nazarin wannan yayin da muke kallon abubuwan ci gaba.

Abin da muka lura da shi shi ne, abin da ya faru a yau ba zanga-zanga ba ce, ba za a iya kare shi ba a karkashin wani jagora, ya kasance laifi ne kamar yadda wasu mutane ke fakewa da sunan zanga-zangar a duk fadin kasar. ”

Ya roki jami’an tsaro da su sanya dokar ta baci tun daga tsakar dare tare da maido da zaman lafiya a jihar.

Yawancin kayayyakin gwamnati da suka hada da tashar jirgin saman Ilorin, Agro Mall, Kwastam da ShopRite Mall da ke Ilorin an lalata su yayin da Palliatives da suka hada da Rice, Yamflour, Indomine da sauran kayan abinci da kayan lantarki da wayoyi da kayan gini wasu ‘yan iska ne suka mamaye wuraren tare da sace su.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.