Barayi Sun haura Sabon massalacin da Aka bude sun sace Gaba daya kayan ciki A Garin Kaduna

 

Wasu barayi da ba’asan ko suwayeba sun Afka wani Sabon massalaci dake unguwar Rafin Guza A yankin karamar hukumar Igabi A jahar Kaduna, Sun sace Gaba daya kayan wiyarin din massalacin cikin Dare.

Mako Guda kenan da bude massalacin barayin sukayi nasarar fasa wani bangare na massalacin suka shiga sukayi ta’asa Aciki.

Lamarin ya tayarda hankalin Al’umma tareda ta’ajibin Abun inda Ake ganin tsantsar rashin imani ne yasa barayi har shiga dakin Allah suyi ta’asa Alokacin da wasu bayin Allah suka bada dukiyarsu Don ginin dakin Allah sukuma sunzo sun sace Don rashin ta’ido.

Daya daga cikin masu lura da massalacin malam sulaiman, Alaramma ya tabbatar Mana da faruwar lamarin inda yayi Allah wadai da Abunda barayin suka Aikata.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.