Rashin iya tsara tattalin Arziki ya sanya Al’umma cikin Talauci–Sarki Sanusi

Tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi 2, ya nuna rashin jindadinsa akan yadda rashin iya tsara tattalin Arziki ya shafi Yan Najeriya wanda ya sanya suke shan wahala.

 

Ya bayyana haka a lokacinda yake kaddamar da jawabi aTaron Saka hannun Jari a Kaduna.

 

A cewar tsohon Babban Gwamnan Bankin Najeriya, rashin iya tsara tattalin Arziki ya shafi yanayin samun da yawa daga cikin Yan Najeriya.

 

Yayi kira ga Gwamnati a dukkanin Matakai dasu yi dubi akan irin yadda matsalolin tsara tattalin arzikin su ya shafi Yan Najeriya.

 

Sanusi ya kuma yi jawabi akan yadda yan Najeriya masu Kudi suka talauce, wanda hakan ya sanya wasu suka dawo da ‘ya’yensu masu karatu kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published.