Gangamin Wayar Da Kan Mata Hausawa Shiga Aikin Soja A Kano, Katsina, Da Jigawa

Kungiyar (save our girl) ta shirya wani Gangami na wayar da kan mata musulmai hausawa dake yankin Arewacin nijeriya musamman A jahohin Kano, Katsina da jahar Jigawa.

 

Kungiyar tayi nazarin yadda wasu ‘kabilu daga kudancin nijeriya suke zuwa jahohin Kano da Katsina da Kuma jigawa suna amfani da sunan hausawa musulmai suna samun Gurbin tafiya Aikin soja Wanda hakan ba ‘karamar barazana bace ga Al’ummar wanan yankin, Ana bawa kowacce jaha adadin mutanen da zata ‘dauka mata da maza Amma saboda matanmu na hausawa basa sha’awar Aikin soja wanan yasa wadanan kabilu suke tururuwar zuwa wadanan jahohi su Sanya sunaye irin na hausawa don su samu Gurbin da za’a bawa wadanan jahohi wanan yasa jahohin Kano ,Katsina da jigawa basa samun isasun wakilai daga

jahohinsu inda ake turo masu wasu kabilu da sunan ‘yan yankin sune saboda matsalar matan hausawa basa son shiga Aikin soja.

 

Kungiyar (save our girl) ta soma Shirin shiga lungu da sako don zakulu matayen da zata wayar musu dakai dakuma nuna musu mihimmancin shiga Aikin soja ga matayenmu na hausawa domin cike Gurbin mataye sojoji na jahohin Kano,Katsina,da jigawa.

 

Gangamin zai fara ne ga mataye masu zaman kansu Wanda suka baro iyayensu suke aikata ayyuka Mara sa kyau maimakon a zuba musu ido wajen ganin suna mummunan ayyuka ‘Kungiyar zata jawo hankulansu wajen ganin Sun shiga Aikin soja Koh don kare martabarsu da Kuma samun mafakar Aikata Abinda suke so ta haka za’a cike Gurbin mataye sojoji da ake bawa jahohin Kano,Katsina da jigawa maimakon Ace wadanda ba kabilun mu ba Kuma ba Addininmu ba suna shiga wanan Aiki da sunan yankinmu da sunan Addininmu gwara mu tura irin wadanan mataye masu zaman kansu zuwa wanan Aikin maimakon mubarsu haka rayuwarsu ta lalace in Akayi sa’a sa zamo nagari hakan yazama silar chanja dabi’unsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.