CORONA: Akwai Yiwuwar Sake Kakaba Dokar Kulle A Najeriya, Inji Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustafah

A daidai lokacin da wasu jihohi suka sake bude makarantun firamare da sakandire, Gwamnatin Tarayya ta yi kira da su kara yin taka-tsantsan saboda kauce wa barazanar sake barkewar cutar COVID-19.

 

Tuni dai aka sake bude makarantu a jihohin Legas, Ekiti da kuma Ogun, yayin da wasu da dama kuma suka saka ranakun komawar.

 

Sai dai gwamnatin ta yi gargadin cewa in ba a yi aiki da lura ba, sake bude makarantun, dawo da sufurin jirage na kasa da kasa da sauran abubuwa na iya mayar da hannun agogo baya kan irin nasarorin da yanzu haka aka samu kan yaki da cutar.

 

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa na yaki da cutar, Boss Mustapha shi ne ya yi gargadin yayin jawabin kwamitin a Abuja ranar Litinin.

 

Ya ce a cikin kusan mako dayan da ya gabata, masana kimiyya na ta kokarin gano musabbabin samun sabbin masu kamuwa da cutar musamman a wasu kasashen nahiyar Turai.

 

Hakan, a cewarsa ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fara nuna damuwarta a kai.

 

Mustapha ya ce hakan ne ma ya tilasta kasar Isra’ila sake sanya dokar kulle ta mako uku.

 

Ya kara da cewa Amurka na duba yiwuwar sanya dokar kulle yayin da Spain ta sanay dokar a birnin Madrid duk da boren ‘yan kasar.

 

Ainihin darasin da Najeriya za ta koya a ciki shi ne duk da nasarar da muka samu, akwai bukatar kara yin taka-tsantsan, mun bude tare da sassauta abubuwa da dama,” inji Mustapha.

 

Ya ce kiran ya zama wajibi ne la’kari da yadda a yanzu mutane ke shakulatin-bangaro da dokokin kiyaye yaduwar cutar kamar sanya takunkumi, bayar da tazara da dai sauransu.

 

Rahotanni dai na nuna cewa jihohi da dama na sake bude makarantun duk kuwa da shawarar da ake basu, ciki har da ta masana harkar lafiya kan fargabar sake barkewar cutar musamman a makarantun gwamnati saboda karancin kayayyakin kariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: