Tarihin Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris

Marigayi Mai martaba sarkin Zazzau, kuma Sarki na goma sha takwas a mulkin daular fulani a lardin zazzau, an haife shi a zariya a cikin shekara ta 1936 kuma shi Dan Malam idrisu auta ne, daya daga cikin ‘ya’yan sarkin zazzau Malam Sambo, wanda ya yi mulki daga shekara ta 1879-1888, ya fito ne daga jinsin gidan sarautar Katsinawa wadda Malam Abdulkarimu sarkin Zazzau ya fara a cikin shekara ta 1844-1846.

Mai martaba ya yi karatunsa a na elementare a Makarantan Elementare na farko da ke kofan Kuyambana cikin Birnin zaria (TOWN SCHOOL 1 ) A shekarar 1947 zuwa 1950. Bayan kammala karatunsa na elementare sai ya shiga Middle school da ke zariya a cikin shekarar 1950 har zuwa 1955. Bayan kammala Middle school a shekarar 1955 sai ya sami ci gaba zuwa, Babbar makarantar koyan aikin malinta ( katsina training collage) a cikin shekarar 1956 zuwa 1957. Bayan gama karatunsa a katsina Training Collage ya samu kyakkyawan sakamako inda ya fito da takardar shaida ta kwarewa a kan aikin malanta. Daga nan ne ya samu koyarwa a karkashin hukumar ilimi da ke karkashin En’en zaria ( Native Authority ) ya karantar a wurare da dama, kamar Hunkuyi, Zariya, Paki, Zangon Aya.
.
Daga nan Maimartaba ya halarci Kos din da ake yi na sanin yadda ake tafiyar da harkar kudade na ( N.A) A makarantan koyan Aikin mulki dake karkashin Jami’ar Ahmadu Bello zariya (Institute of Administration, kongo A. B. U zaria a cikin shekarar 1961. Bayan ya kammala wannan kos kuma ya sami takardar shaida mai kyau, sai ya fara aiki a karkashin ofishin Marigayi sarkin zazzau Alh. Muhammadu Aminu, a matsayin sakataren sarki ( Private Secretary ). Alh. Shehu Idris ya sake komawa ma’aikata a shekarar 1963 , da gamawarsa ne sai ya shiga aikin gwamnatin Jahar Arewa.

Maimartaba sarkin zazzau Alh. Shehu Idrisu ya kara himmatuwa kan neman ilimi ya tafi kasar Australia don yin kos a kan koyon aikin mulki 1967. Bayan dawowarsa daga wannan kos sai aka bashi Hakimin Birnin Zariya da kewaye kuma aka nada shi sarautar Dan Madamin Zazzau a cikin shekarar 1973.

Yana nan a wannan matsayi na Hakimin Birni Allah ya yi wa Alh. Muhammadu Aminu Rasuwa. Daga nan aka zabi Alh shehu Idrisu ya zama sarki a ranar 8 ga Febrairu, 1975, ya zama sarki na 18 a zazzau na hudu a gidan sarautar Katsinawa. Ya hau gadon sarautar zazzau yana da shekara talatin da tara a duniya yanzu kuma shekaransa 42 a kan gadon sarautar zazzau. Ya hau gadon sarautar zazzau yana da matan Aure guda uku ‘ya ‘ya biyar. Daga baya ya auri diyar sarkin Musulmi Abubakar III a lokacin da ya hau mulki.
.
JERIN SUNAYEN MATAN SA
1. Hajiya Habiba
2. Hajiya Fatima
3. Hajiya Binta
4. Hajiya Mariya
.
Marigayi Alh. Aliyu Shehu , Madakin zazzau , da Marigayi Ahmad Shehu. Mata kuwa su ne Hajiya salaha, Hajiya Aminatu da Hajiya Mairo. Wanda aka fara haifuwarsa a kan gadon sarauta shine Muhammadu Kabiru yanzu haka dai Maimartaba yana da ‘ya’ya Talatin da biyar maza da mata banda wadanda suka rasu.
.
Kamar yadda aka fada a baya cewa madakin zazzau Aliyu shi ne babban Dan sarkin zazzau Shehu , bayan rasuwar madaki nd aka nada Malam kabiru shehu sarautar madaki.. Wanda ya fara rasuwa a maza shine Malam Ahmadu, sai mu’azu sai Madaki Aliyu sai Kabiru, haka kuma a cikin ‘ya ‘yan Sarki mata wadda ta fara rasuwa ita ce Haj zaliha, matar Alh Ja’afaru. Muna fata Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, yasa muma idan namu ya zo mu cika da imani. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.