Ya Kamata Farashin Man Fetur Ya Yi Sauki Idan Har Da Gaske An Cire Masa Tallafi, Cewar Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicinsa game da ƙarin kuɗin man fetur da gwamnati ta yi.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyaer adawa ta PDP ya ce indai da gaske an cire tallafi to ya kamata man ya yi sauƙi.

Atiku ya ƙara da cewa ko kusa ba ya goyon bayan ƙarin kuɗin man kuma yana kallon abubuwan ne a matsayinsa na ɗan kasuwa, wanda yake hangen abubuwa ta fuskar tattalin arziki.

Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Talata, yana mai cewa farashin man fetur a Turai da Amurka ya ragu kan yadda yake a 2019.

“idan har da gaske gwamnati ta cire hannunta daga kasuwancin man, to ba kamata ya yi a ce ya yi sauƙi ba?” In ji Atiku.

Leave a Reply

Your email address will not be published.