Talauci Da Lalacewar Tattalin Arziki Karuwa Yake A Kowacce Rana A Nijeriya, Cewar Osinbajo


Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jajanta halin talaucin da kasar nan ke ciki tare da karairayewar tattalin arziki hadi da matsin rayuwa da annobar korona ta ke janyowa a kullum, da yake karuwa a kowacce rana a fadin kasar.

Kamar yadda ya sanar a wata takardar da ya fitar a ranar Talata hannun kakakinsa, Laolu Akande, mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin taron duba yanayin aikin ministoci na shekara da da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Kamar yadda taken takardar ya bayyana, “Mataimakin shugaban kasa ga ministoci: Bukatar gaggauta amfani da kudin rage radadin da gwamnati na ware.

A takardar, mataimakin shugaban kasa ya ce, “A halin yanzu muna rana ta 67 tun bayan fara shirin. Babu abinda zai faru kamar sihiri, dole ne mu yi komai da kanmu.

Dole mu tabbatar da cewa muna da kudin kuma muna duba ci gaban da ake samu a kowacce rana. Ta hakan ne za’ayi abinda ya dace a lokaci da ya dace.

Hakazalika, lokaci ba zai sassauta mana ba. A kowacce rana talauci karuwa yake kuma tattalin arziki na sake yin kasa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.