Sojoji Sun Yi Nasarar Kashe Gawurtaccen Dan Ta’addan Da Ya Addabi Jihohin Benue, Nasarawa Da Taraba

An yi nasarar murkushe wani dan ta’adda mai suna Gana, wanda ya addabi al’ummar jihohin Taraba Nasarawa da Benue da wasu sassan kasar nan.

Shi dai Gana kowa ya san shi da dabi’ar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Jami’an tsoro sun jima suna farautar sa inda a jiya suka yi nasarar bindige shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.