Matashin Da Aka Yankewa Hukuncin Kisa Saboda Batanci Ga Annabi (S.A.W) Ya Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli

Bangaren shari’a na jihar Kano ya ce matashin nan da wata Kotun Shari’ar Musulunci ta yanke wa hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi Muhammadu SAW ya daukaka kara a yau.

Hakan na nufin cewa ya tsallake siradin zartar masa da hukunci matukar ya wuce kwanaki 30 bai daukaka kara ba kan hukuncin da aka yanke masa ba.

A jiya ne shahararren lauyan nan mai kare hakkin bil adama Femi Falana ya ce kotun ta Kano ta hana takardun shari’ar, wadanda za su ba da damar daukaka kara, to sai dai kotun ta musanta zargin.

Baba Jibo Ibrahim shi ne kakakin kotunan Kano, kuma abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya tambaye shi karin bayani kan batun daukaka karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: