Buhari ya bada umarnin fitar da ton dubu 30,000 na Masara

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce ya bada umarnin fitar da Ton dubu talatin (30,000mtons) na masara ga manoma a faɗin ƙasar nan daga ma’adanan abincin gwamnati.

Buhari ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter Hausa Daily Times ta ruwaito.

Ya bayyana cewa, hakan zai saukaka tsadar da yanzu ake samu na kiwon kaji tsakanin masu samar da abincin dabbobi.

“Muna sane da irin tsada da kayan abinci ya yi, a lokacin da tattalin arzikin duniya ke tangal-tangal bisa bullar annobar Corona Virus, muna yin iya bakin kokarin mu domin faɗo da farashin kayan abinci a fadin kasar nan” a cewar jawabin da aka wallafa a shafin shugaban kasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: