Ba Mu Mori Gwamnatin Buhari Da Komai Ba, Cewar Matasan Arewa

Wasu bayin Allah sun fito cikin makon nan suna jimami tare da kalubalantar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta nuna ayyukan da ta yi a Arewa.

Ƴan Arewacin Nijeriya su ne suka fi bada kaso mai tsoka a tafiyar jam’iyyar APC, saidai kuma wasu Matasan yankin suna ganin babu abin da yankin Arewa ya amfana.

Wadannan matasa sun fito kan dandalin sada zumunta su na kalubalantar gwamnatin APC ta bayyana irin moriyar da su ka ci tun da aka kafa gwamnati a 2015.

Wasu Kuma suna zargin cewa akwai yaudara a lamarin gwamnatin APC, ganin yadda ake fama da rashin tsaro da kuma tsadar kayan abinci, game da darajar Naira da ta karye.

Haka zalika wasu kuma sun rika bankado irin gudumuwa da goyon bayan da su ka bada wajen hawan shugaba Buhari mulki a 2015, su na yi masa gorin cewa anyi Watsi Dasu.

Wasu Matasan Sunce Goodluck Jonathan ya yi wa Arewacin Aiki Najeriya fiye da abin da Buhari da su ka zaba ya yi masu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: