An Kusa Halaka Mutumin Da Aka Kama Yana Fyade A Masallaci


Yanzun nan aka kama wani mugun mutumi a Wunti Street cikin birnin Bauchi, ya ja yarinya karama ‘yar shekara 4 cikin Masallaci yayi mata fyade, ya lalata farjin yarinyar tana ta zubar da jini, an garzaya da ita zuwa Asibitin koyarwa na Sir Abubakar Tafawa Balewa University Teaching Hospital (ATBUTH).

Mutanen unguwa sun masa dukan tsiya kafin isowar ‘yan sanda, da ake tuhumarsa ya bayyana cewa abin nasu kungiya ne, sun kai su 5 da suka bazu a unguwannin Bauchi, kuma kungiyar tace a cikin Masallaci ake da bukatar suyi fyaden, asalinsa mutumin unguwar Yakubu-Wanka ne a cikin garin Bauchi

Ya kai kusan kwana 5 a Wunti Street yana ta wasa da yara kanana mata yana raba musu kudi da minti, kafin yau ya yaudari ‘yar shekara 4 zuwa cikin Masallaci ya yi mata fyade, Yanzu haka yana State CID Bauchi

Allah Ka kawo mana karshen wannan masifa. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: